(ABNA24.com) Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, karuwar rashin tsaron ya yi sanadiyyar kawo tsaiko wajen gudanar da ayyukan jin kan bil Adama.
Kasar ta jima tana fama da hare haren kungiyoyin masu ikirarin jihadi.
Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD OCHA ya sanar da cewa, dukkan shiyyoyi 13 na kasar a halin yanzu suna fuskantar hare hare, inda mutanen da rikici ya raba da muhallansu kashi 90% ke rayuwa a cikin unguwannin da aka kebe domin tsugunar da su.
Matsalar karancin abinci ita ma na ci gaba da karuwa a yankunan, in ji ofishin hukumar OCHA.
342/